Zan ba ilmi da ci gaban matasa muhimmanci idan na zama shugaban kasa – Kwankwaso
Zan ba ilmi da ci gaban matasa muhimmanci idan na zama shugaban kasa – Kwankwaso
Dan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya lashi
takobin ba bunkasa ilmi da gina matasa muhimmanci idan ya zama shugaban kasa a
zaɓen 2023.
Rabi’u Kwankwaso na magana ne a Kano a lokacin kaddamar da ofishin yakin neman
zaɓen shugaban kasa, inda ya ce matasa zansu murmusa a ci gaba da karatu a
makarantun boko a duk fadin kasar. Ya yi nuni da cewa babu kasar da za ta ci
gaba, ba tare da ba ‘yan kasar ilmi mai inganci ba da hakan zai ba su damar
hidimta wa kasar.
Comments
Post a Comment