BA ZA A SOKE ZABEN 2023 DIN NAN BA-MINISTAN LABARU LAI MUHAMMED
BA ZA A SOKE ZABEN 2023 DIN NAN BA-MINISTAN LABARU LAI MUHAMMED
Ministan yada labarai na Nigeria |
Ministan labarun Najeriya Lai Muhammed ya ce ba za a soke babban zaben 2023 da za a gudanar a ranar 35 ga ‘yan takarar shugaban kasa da majalisar dokokin taraiya sai kuma ranar 11 ga watan Maris a gudanar da zaben gwmanoni da ‘yan majalisar jiha.
Lai Muhammed na magana ne a cigaba da tarukan ambata irin aiyukan da gwamnatin Buhari ta gudanar inda ministoci kan baiyana su ambata aiyukan da ma’aikatun su su ka cimma.
Ministan na fadar matsayin gwamnatin Najeriya bayan bayanin jami’in hukuamr zabe Abdullahi Zuru da ke cewa matukar ba a inganta tsaro ba za a iya soke zaben ko dage shi.
Ministan ya ce gwamnati ta shirya don tabbatar da gudanar da zaben da kuma aiyana wanda zai lashe zaben.
Lai Muhammed ya kara da cewa ya san hukumar zabe wato INEC a takaice na aiki da jami’an tsaro don samar da yanayin gudanar da zaben.
Hare-hare kan ofisoshin hukumar zabe a musamman jihohin kudu maso gabar ya sanya shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ya nuna fargabatar nasarar aiwatar da zaben.
Comments
Post a Comment