MUN YI NASARAR BUDE KOFAR TATTAUNAWA TSAKANIN SOJAN NIJAR DA TINUBU- TAWAGAR MALAMAI

MUN YI NASARAR BUDE KOFAR TATTAUNAWA TSAKANIN SOJAN NIJAR DA TINUBU- TAWAGAR MALAMAI

 


Tawagar manyan malaman Islama na Najeriya da ta gana da shugaban gwamnatin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ta aiyana nasarar ziyarar.


Malaman sun ce ganawar ta ba su damar bude kofar tattaunawa tsakanin sojojin da shugaba Tinubu da kuma kungiyar ECOWAS.


Jagoran tawagar ce Sheikh Abdullahi Bala Lau ya baiyana muhimmancin amfani da tsoffin shugabannin kasa da manyan malamai da a ke mutuntawa a Najeriya da Nijar don samar da maslaha.

 


Shaharerren malamin ya ce da yardar Allah bayan ganawar su da shugaba Tinubu za a samu matsaya mafi a'ala ga dukkan bangarorin don matakin soja ba zabi ba ne a wannan yanayi.


Da ya ke karin bayani Farfesa Mansour Sokoto ya ce ko da irin karramawar tarba da tawagar ta samu ya nuna an kama hanyar sulhu mai dorewa.

 


Ta bakin Farfesa Sokoto, shugaban Sojan Janar Tchiani ya ba da hakurin rashin ganawa ta kai tsaye da tawagar ECOWAS.


A tawagar akwai Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, Farfesa Salisu Shehu da 

Comments

Popular posts from this blog

RIKICHIN YA BARKR AKAN HAKAR MA ADANAI STAKANI ADAMAWAN DA TARABA

Rundunar Yan Sandar Jihar Adamawa Dun Kashe Mutane Shidda Masu Garkuwan Da Mutane